Faransa za ta kori al'ummomin Roma da ke zaune a kasar ba da izini ba

Al'ummomin Roma
Image caption Al'ummomin Roma

Gwamnatin Faransa zata bullo da wasu jerin matakai na takaita yawan al'ummomin Roma wadanda basa zama wuri guda, da nufin korar dukan wadanda suke zaune a yankunan kasar ba tare da izini ba.

Ministan harkokin cikin gida na Faransa, Brice Hortefeux, ya ce za a cire rabin sansanonin da wadannan al'ummomi na Roma ke amfani da su a cikin watanni ukku masu zuwa.

Wannan sanarwa ta zo ne a karshen wani taron gaggawa na majalisar ministoci, wanda shugaba Nicolas Sarkozy ya kira, domin tattaunawa a kan tarzomar makon jiyar da al'ummomin Romar suka yi a tsakiyar Faransa.

Shugaba Sarkozy yayi Allah wadai da halayyarsu, yana mai cewar, alhakin kare doka ya rataya a wuyan al'ummomin Romar kamar yadda ya rataya a wuyan 'yan asalin kasar Faransa.