Tarihin Nijar a takaice

Bare Mai Nasara
Image caption Tsohon shugaban Sojin Nijar Bare Mai Nasara

Muhimman Abubuwan da suka wakana a jamhuriyar Nijar

Jamhuriyar Nijar ta samu 'yancin kai daga Turawan mulkin mallaka na Faransa a shekara ta 1960, bayan da Turawan suka shafe shekaru suna mulkin kasar.

1890 - Turawan Faransa suka mamaye Nijar.

1958 - Nijar ta zamo jamhuriyar mai kwarya-kwaryan cin gashin kai karkashin Faransa.

1960 - Nijar ta samu 'yancin kai; sannan an yi zaben majalisun dokoki, inda aka zabi Diori Hamani shugaban kasa.

1968-73 - Mummunan fari ya afka wa amfanin gonar kasar.

1974 - Sojoji sun kifar da gwamnatin Diori Herman a wani juyin mulki karkashin jagorancin Laftanal Kanal Seyni Kountche.

1987 - Ali Seybou ya maye gurbin Kountche wanda ya rasu sakamakon cutar sankarar kwakwalwa.

1989 - An samar da sabon tsarin mulki wanda ya maida kasar kan tafarkin dimokradiyya, amma karkashin jam'iyya guda; inda aka sake zaben Seybou a matsayin shugaban kasa.

Image caption Jamhuriyar Nijar ta yi fama da juyin mulki daban daban a tarihi

Dage takunkumi kan jam'iyyun siyasa

1990 - Kungiyoyin kwadago da dalibai sunyi ta kiran da a baiwa jam'iyyun adawa damar shiga a dama da su a harkokin siyasar kasar.

Matsin lambar tasa a shekarar 1990, shugaba Seybou ya dage takunkumin hana jam'iyyun adawa a kasar.

Har ila yau a shekarar 1990 ne kuma, al'ummar Abzunawa suka fara bore a yankin Arewacin kasar.

1991 - Wannan yasa aka kafa sabbin jam'iyyun adawa da kungiyoyin fararan hula da dama, abinda ya sa aka kaddamar da wani babban taron kasa wato Conference Nationale a watan Yulin shekarar 1991.

A taron aka samar da sabon kundin tsarin mulkin da ya tsige shugaba Ali Seybou, aka kuma nada Andre Salifou a matsayin shugaban rikon kwarya har sai lokacin da aka gudanar da zabe.

1992 - Majalisa ta sa hannu kan sabon kudin tsarin mulkin kasar wanda ya kai Nijar Jamhuriya ta uku a shekarar 1992.

1993 - A shekarar 1993, an gudanar da zabe inda Mohamman Ousman ya lashe zaben shugaban kasa karkashin tutar jam'iyyar CDS Nasara, wacce ta lashe kujeru masu rinjaye a majalisar dokokin kasar.

1995 - A shekarar 1995, an kulla yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin gwamnati da 'yan tawayen Abzunawa wadanda ke bore a Arewacin kasar.

Image caption Dauda Malam Wanke ya shugabanci Nijar ta hanyar soji a shekarar 1999

Karin juyin mulki

1996 - A shekarar 1996, Kanal Ibrahim Bare Mainasara, ya jagoranci kifar da gwamnatin Mohamman Ousman bayan da aka samu rikici tsakanin shugaban kasa da Fira Minista a shekarar 1995, kan zaben majalisar dokokin da aka gudanar.

A watan Mayu na 1996, Kanal Bare ya nada wani kwamiti da zai sauya kundin tsarin mulkin kasar, wanda aka amince da shi bayan kada kuri'ar jin ra'ayin jama'a, abinda ya kai kasar ga jamhuriya ta hudu.

A watan Yuli na 1996, Kanal Bare ya lashe zaben shugaban kasar da ya shirya, abinda ya bashi damar ci gaba da kasancewa shugaban kasa, har zuwa watan Aprilun shekarar 1999.

1999 - A watan Aprilu na 1999, aka kashe Kanal Bare a wani juyin mulki da masu tsaron lafiyarsa suka aiwatar, inda Manjo Daouda Malam Wanke ya karbi shugabancin kasar.

Bayan hawansa mulki a wannan shekarar ne Manjo Dauda Malam Wanke ya kafa wani kawamiti da zai sa ido kan rubuta sabon kundin tsarin mulkin da ke da yanayin tsarin mulkin Faransa da na shugaba mai cikakken iko.

Image caption Shugaban Tandja ya fuskanci suka daga kasashen duniya da dama

Kuma a watan Agusta na shekarar 1999 ne aka amince da sabon tsarin mulkin a wata kuri'ar jin ra'ayin jama'a da aka kada.

A watannin Oktoba da Nuwamba na 1999, an gudanar da zaben da masu sa ido na ciki da wajen kasar suka ce an yi shi cikin gaskiya da adalci, kuma jam'iyyar MNSD ce ta lashe zaben, wanda ya dora Mammadou Tandja kan karagar Mulki.

2001 - An sanya dokar hana farautar namun daji da suka hadar da Zaki, barewa, da sauransu.

2002 - A shekara ta 2002, sojoji suka yi bore a gabashin kasar da kuma babban birnin Yamai, domin neman a biya su albashinsu da kuma kyautata rayuwarsu.

Zargin Uranium

2003 - A watan Janairu, shugaba Bush na Amurkaya yi zargin cewa, kasar Iraki ta yi kokarin sayen makamashin Uranium daga Nijar don habaka shirinta na samar da makamashin Nukiliya. An kuma yi makamancin wannan zargin a wata takardar bayanai ta kasar Burtaniya a watan Satumbar shekarar 2002 a kan Iraki.

A watan Maris, hukumar majalisar dinkin duniya mai kula da makamashin Nukiliya ta ce, bayanan da kuma kundayen da aka fitar kan alakar Nijar da shirin Nukiliyar Iraki, na karya ne, ba su da tushe balle makama.

2004 - A watan Yuli, an yi zaben kananan hukumomi a karon farko. Jamiyyun da ke mara wa shugaban kasa ne suka lashe zaben da gagarumin rinjaye.

2004 - A watan Disamba, shugaba Tandja ya lashe zabe a karo na biyu da kashi 65.5 cikin dari a zagaye na biyu na zaben.

2005 - A watan Maris, an soke wani biki da aka shirya yi na samun 'yanci ga wasu bayi 7,000, saboda hukumomi sun ce babu bayi a kasar.

2005 - A watan Yuli, majalisar dinkin duniya ta yi gargadin cewa, miliyoyin mutane na fama da matsalar rashin abinci mai gina jiki saboda karancin abincin da ya shafi kasar sakamakon fari da kuma farin dango da suka yi wa amfanin gona barna.

2006 -

2009 - Mayu-Yuni - Shugaba Mamadou Tandja ya dakatar da amfani da tsarin mulki bayan da kotun tsarin mulkin kasar ta yi watsi da bukatarsa ta neman tazarce.

2009 Augusa - Kuri'ar jin ra'ayin jama'a mai cike da cece kuce da a ka gudanar ta amince da sabon tsarin mulkin, wanda ya baiwa shugaban damar ci gaba da mulki da kuma karin iko.

2009 Octoba - 'Yan adawa suka kaurace wa zaben majalisar dokokin da aka gudanar domin maye gurbin majalisar da Tandja ya rusa. Magoya bayansa sun lashe zaben da gagarumin rinjaye.

Hukumar kula da ci gaban tattalin arzikin kasashen Yammacin Afrika ECOWAS, ta dakatar da Nijar bayan da gudanar da zaben.

Image caption Shugabannin mulkin sojin Nijar sun yi alkawarin gudanar da zabe a watan Fabreru

2010- February - Sojoji suka kifar da gwamantin Tandja, inda aka nada Kanal Salou Djibo, ya jagoranci majalisar gwamnatin sojin kasar. Kungiyar Tarayyar Afrika ta dakatar da Nijar daga kungiyar.

2010- Maris - Shugaba Salou Djibo ya yi alkawarin maido da kasar kan tafarkin dimokradiyya, amma ba tare da sanya ranar zabe ba.

Majalisar sojin ta kafa gwamnatin riko karkashin jagorancin Fira Ministan farar hula Mahamadou Danda.

2010 Mayu - Kungiyoyin agaji suka ce karancin abinci na fuskantar kimanin mutane miliyan bakwai ciki harda kananan yara.