Nijer da bankin raya kasashen Afrika sun kulla yarjejeniya

A jamhuriyar Niger, hukumomin kasar da bankin raya kasashen Africa ta yamma, Beo -wa-de/ West African Development Bank, sun sanya hannu a kan wata yarjejeniyar gina wata hanyar mota mai suna Niamey- Walam, wadda za ta hada kasar ta Nijar da makwabciyarta, kasar Mali a kokarin bunkasa al'ummomi da dukiyar mazaunan wannan yanki.

Aikin gina hanyar dai zai ci kudi Bilyan hudu da rabi na CFA.

Baya ga wanna aiki dai, bankin na kuma taka wata muhimmiyar rawa a cikin ayyukan gina gandari ko filayen noma na zamani domin yaki da matsalar karancin abinci a Niger harma da wasu sauran kasashen yankin Africa ta Yamma.