Nijeriya zata hukunta kamfanoni kan hannayen jari

Mahukunta a Nijeria sun ce zasu gurfanar da wasu kamfanoni da mutane da suka kai dari biyu da sittin zuwa gaban wata kotu ta musamman a bisa zargin yin wasu abubuwan da suka sabawa doka a kasuwar hada-hadar hannayen jari ta kasar.

Ba'a dai bayyana sunayen wadanda ake zargin ba, to amma sun kama daga dillalai a kasuwar da akantoci da kuma lauyoyi.

Ana dai zarginsu ne da aikata laifukan da suka shafi harkokin tattalin arziki, kamar zamba, da daidaita farashin hannayen jari da fitar da cinikin sirrin kasuwa.

Wakiliyar BBC a Nigeria ta ce, rikicin bankunan da aka fuskanta a Nigeriar a bara, ya bankado abubuwa da dama da ake yi ba daidai ba a kasuwar hannayen jarin ta kasar.

Ta ce a daidai lokacin da wasu bankunan Nigeriar suka kai gab da durkushewa, sai abu ya fito fili cewar rashin ingantattun dokoki da kuma rashin sa-ido sosai akan yadda dillalai ke gudanar da harkokin su a kasuwar hada hadar hannayen jari na daga cikin manya manyan matsalolin da ake fuskanta.