Jam'iyyar ANPP ta dage babban taron ta

Image caption Farfesa Attahiru Jega

Jam'iyyar Adawa ta ANPP

A Najeriya jam'iyyar adawa ta ANPP, ta dage babban taronta da ta shirya yi a karshen makon nan, domin zaben sabbin shugabannin jam'iyyar da kintsawa zabubbukan dake take tafe.

Daga babban taron dai ya biyo bayan jan kunnen da hukumar zabe ta kasa, ta yiwa jam'iyyar ne cewa, bata cika ka'idojin yin taron ba.

Honorable Ali Ndume ya fadawa BBC cewa, za'a guidunar da babban taron a ranar sha shida ga watan satumba.

Da ma dai an zurawa wannan babban taro na jam'iyyar ta ANPP ido, domin ganin yadda zata warware matsaololin da suka yi mata dabaibayi.