Jam'iyyar ANPP ba ta da ra'ayin karba-karba

Taswirar Najeriya
Image caption Taswirar Najeriya

A Najeriya, jam'iyyar adawa ta ANPP ta bayyana cewa, ba ta da niyyar kebe damar tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2011 ga wani bangare na kasar.

Wannan dai ya biyo bayan wani taro ne da shugabannin jam'iyyar suka gudanar, inda suka tattauna a kan batutuwa da dama, ciki har da batun kebe kujerar dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar ga arewacin kasar.

Masu son dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar ta ANPP ya fito daga arewa dai na ganin hakan zai sake karfafa jam'iyyar, bayan raunin da ta yi sakamakon ficewar wasu jiga-jiganta da suka hada da Janar Muhammadu Buhari mai ritaya, da kuma wasu gwamnonin jihohi na yankin.