Firayim Minista Cameron ya kafe kan kalamansa game da Pakistan

Image caption Mista David Cameron

Firayim ministan Biritaniya, David Cameron, ya kare kalaman da ya yi ranar Laraba - inda ya zargi wasu a Pakistan da goyon bayan ta'addanci.

Ya ce aikinsa ne ya fadi gaskiya, ya kuma fade ta karara.

Sai dai Jakadan Pakistan a Biritaniya, Wajid Shamsul Hassan, ya ce kungiyoyin da suke ayyukan ta'addanci a halin yanzu, Amurka da kawayenta ne suka kafa su lokacin da suke gaba da Tarayyar Soviet a shekarun 1980.

Ya ce, "Su ne suka samo 'yan mujahiden suka kuma shigar da su Pakistan da Afghanistan domin su ci gaba da yaki da Tarayyar Soviet."