Hasarar rayuka a hadarin jirgin ruwa a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo

Jirgin ruwa a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo
Image caption Jirgin ruwa a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo

Mutane akalla 80 sun hallaka a wani hadarin jirgin ruwa a jamhuriyar Demokradiyyar Congo.

Jirgin ruwan na dauke da mutane kimanin 200 da suka hada da pasinjoji da kuma ma'aikatan jirgin.

Rahotanni sun ce, hadarin ya auku ne a wata magama dake kan kogin Congo, a ranar Laraba, amma sai yanzu ne ake kara samun bayyanai.

Har yanzu babu cikakken bayani kan musabbabin hadarin, amma an ce jirgin ruwan na makare da jama'a, yayinda ruwan kogin kuma ya ja kasa sosai.

Masu aikin ceto na cigaba da neman wadanda Allah yayi wa gyadar dogo.