A yau David Cameron zai gana da firaministan India

Image caption Mista David Cameron

A yau David Cameron zai gana da Firaministan India

Firaministan Burtaniya David Cameron zai gana da takwaransa na India Manmohan Singh nan da yan sa'o'i kadan a rana ta karshe ta ziyarar da ya kai kasar wacce ta samu cikas bayan wani sabanin diplomasiyya tsakaninsa da Pakisatan mai makwabtaka da Indiyan.

A ranar Laraba ne dai Mr Cameron ya baiyana abinda ake gani tamkar suka ne ga Pakistan na tallafawa aiyukan ta'addanci, kwanaki kadan bayanda aka yayata wani rahoton sirri na sojin Amurka da ya baiyana alaka tsakanin jami'an leken asirin Pakistan da mayakan Taliban a Afghanistan.

Batun ya janyo martani mai zafi daga jakadan Pakistan a Burtaniya Wajid Shamsul Hasan wanda ya zargi Mr. Cameron da iza wutar rikici a yankin.