Majalisar tuntubar juna a Nijar ta fara wani muhimmin zama

Shugaba Salu Jibo na Nijar
Image caption Shugaba Salu Jibo na Nijar

A Jamhuriyar Nijar,majalisar tuntubar juna, CCN, ta fara wani zama na kwanaki goma sha biyar, inda za ta yi muhawara game da kundin tsarin mulkin da ya dace da kasar.

A halin da ake ciki dai, majalisar mulkin sojn kasar ta CSRD, ta gabatar wa majalisar tuntubar junan wata shawara ta tsarin mulki mai ruwa biyu.

Wannan tsarin mulki dai na raba iko ne tsakanin shugaban kasa da Firayim Minista.

A kwanaki baya ne kuma kawancen AFDR, da ya mulki kasar ta Nijar a baya, ya gabatar da wata shawarar mai son ganin an baiwa shugaban kasa cikakken iko.