An rusa kwamitin sadarwa na majalisar dattawan Najeriya

Majalisar Dokokin Najeriya
Image caption Majalisar Dokokin Najeriya

Shugaban majalisar dattawan Najeriya, David Mark, ya rushe kwamitin sadarwa na majalisar, bayan zargin da aka yi na wata badakala dangane da tantance sabbin shugabannin hukumar sadarwa ta kasa, NCC.

Shugaba Goodluck Jonathan ne ya mika wa majalisar sunayen sabbin shugabannin hukumar domin neman amincewar ta.

Badakalar ta taso ne bayan wani wakili a kwamitin sadarwa na majalisar dattawan yayi zargin cewar, bada saninsu ba shugaban kwamitin ya rubuta rahoton cewa, kwamitin ya tantance sabbin shugabannin hukumar ta NCC.

Shugaban kwamitin da aka rusa bai ce komai ba dangane da lamarin.