Ana zaman makokin a Pakistan

'Yan uwan wadanda hadarin ya  auku da su
Image caption 'Yan uwan wadanda hadarin ya auku da su

Kasar Pakistan tana zaman makoki na kwana guda domin jimamin wadan da suka rasa rayukansu a hadarin jirgin sama mafi muni a tarihin kasar.

Jirgin saman kirar Airbus A321 ya fadi ne a babban birnin kasar, Islamabad, inda mutane 152 da ke cikin sa suka halaka.

Jirgin wanda ya taso daga kudancin karaci na daya cikin jiragen shararren kamfanin nan na Airblue a Pakistan.

Har yanzu dai ba a gano musababin hadarin ba wanda ya faru a yayin wani ruwan sama mai karfi.

Jirgin dai na dauke na fasinjoji 146 da kuma ma'aikata shida a lokacin da ya yi hadarin a yankin tsaunukan Margalla.

Firayim Minista Yousuf Raza Gilani ya sanar da ranar alhamis ta zama ranar makoki, kuma ya bada umarnin sauko da tutoci kasa-kasa a duk fadin Pakistan.

Zaku kuma kallon hotunan faduwar jirgin sama http://www.bbc.co.uk/hausa/multimedia/2010/07/100728_pakistan_crash_gallery.shtml

Ministan yada labarai a Pakistan Qamar Zaman Kaira ya ce kawo yanzu an gano gawawaki 115 amma, amma ana kokari a fiddo da ragowar daga yankin mai sarkakiya.

Aamir Ali Ahmed, wani babban jami'in gwamnati ya shaida wa kamfanin dilanci labarai na Reuters cewa ruwan saman da aka yi kamar da bakin kwarya ne ya kawo jinkirin tsinto gawawakin.

Wani mai aikin ceto Dawar Adnan ya shaida wa kamfanin dilancin labarai na Associated Press cewa sassan jiki na fasinjojin jirgin na baje a inda jirgin ya fadi, sassan da wuya a iya gane ko na wane da wane.

Ofishin jakadancin Amurka a Pakistan ya ce akwai Amurkawa biyu a cikin jirgin amma basu bada karin bayani akai ba.

Jami'an da ke binciken sun ce har yanzu ba a gano na'urar daukan bayanai da ake kira black-box ba, yayin da suke karyata rahotannin da ke cewa an samu na'uran.

Wakilin BBC a Islamabad Aleem Maqbool ya ce an hana jirage tashi daga Islamabad zuwa Kabul saboda rashin kyawun yanayi.

Jama'a dai na ci gaba da tambaya game da dalilan da suka sanya aka bari jirgin ya tashi duk da sanin cewa yanayin da ya tashi a ciki ba shi da kyau.

Image caption Taswiran inda hadarin ya auku