Zan tsaya takarar shugaban Najeriya -inji Shekarau

Zaben shugaban kasar Najeriya

A Nigeria gwamnan jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin kasar a karkashin tutar jam'iyyar adawa ta ANPP. Gwamnan ya musanta cewa yana fuskantar matsin lamba daga jam'iyyarsa kan ya barwa wani wannan takara, inda yace babu wanda ya taba tunutubarsa kan batun.

Dama dai an jima ana jita jitar cewa gwamnan na Kano yana da sha'awar yin takarar, musamman duba da yadda makusantansa ke ta kiraye kirayen ya fito.

To amma wasu jama'ar jahar ta Kano na da ra'ayin cewa da gwamnan ya gane da bai dauki wannan mataki ba, domin sunce ba shi da karfin gwiwar da zai iya mulkar Najeriya bisa zargin cewa yana kau da kai ga wasu laifukan da wasu makusantansa ke aikatwa.