An bankado 'yan damfara a jahar Sakkwato

'Yan sandan Najeriya
Image caption 'Yan sandan Najeriya

A Najeriya rundunar 'yan sandan jihar Sakkwato ta ce ta yi nasarar kama wani mutum mai suna Chukwu Obinna, wanda take zargi da hannu a damfarar jama'a, bayan da ta bankado asirin wani kampani na boge.

Kampanin na karyar cewa yana aiki ne da Majalisar Dinkin Duniya.

Yana gayyatar mata daga sassa daban daban na Najeriyar, da zummar daukarsu aiki, amma daga bisani ya yaudare su.

A 'yan kwanakin nan dai an yi ta samun rahotannin bullar kampanoni na boge, wadanda ke damfarar jama'a a sassa daban daban na arewacin Najeriyar.