An zartar da kudurin samar da tsabtattacen ruwan sha a duniya

An zartar da kudurin samar da tsabtattacen ruwan sha

Babban zauren majalisar dinkin duniya ya zartar da kudirin da ya bayyana samar da tsabtataccen ruwa da ingantaccen mahalli a matsayin hakkin bil adama duk da kauracewa kuri'ar da kasashe arba'in suka yi ciki har da Burtaniya da Amurka.

Wasu daga cikin kasashen da suka ki marawa kudirin baya sun nuna damuwa ne kan gaza tantance nauyin da ke kansu da kudirin ya yi, yayinda wasu kuma su ka yi fargabar kudirin zai iya kafar ungulu ga wata yarjejeniyar da kasashen duniya ke kokarin cimma akan samar da ruwan shan a yanzu haka a Geneva.

wakiliyar BBC tace kusan mutane biliyan guda ne ke rashin tsabtataccen ruwan sha.

Mutane biliyan biyu da miliyan dari shida kuma na rayuwa ne cikin kazanta yayinda kananan yara miliyan daya da rabi ne ke rasuwa a kowace shekara sanadiyyar cututtukan da suka danganci kazanta da rashin ruwa mai tsafta.