Amurka ta nuna fushinta dangane da bayanan sirri

yaki
Image caption Sakataren tsaro Amurka da shugaban kasar Afghanistan

Amurka ta fusata

Manyan jami'an gwamnatin Amurka sun baiyana fushinsu bisa yayata takardun sirrin soji guda dubu casa'in dangane da yakin Afghanistan .

Sakataren tsaro Robert Gates, ya bayyanawa yan jarida a fusace cewa, hakan na iya jefa rayukan sojin Amurka da na kasashen kawance da kuma dakarun Afghanisatan masu mara masu baya cikin hadari.

A nasa bangaren babban hafsan sojin Amurka, Admiral Mike Mullen ya ce jinin sojin Amurka na wuyan Julian Assange wanda ya yayata bayanan a shafinsa na Intanet, wikileaks.