Jam'iyyar ANPP ta dage babban taronta

Image caption Farfesa Attahiru Jega

Jam'iyyar Adawa ta ANPP ta dage babban taronta

A Najeriya jam'iyyar adawa ta ANPP ta dage babban taronta da ta shirya yi a karshen makon nan domin zaben sabbin shugabannin jam'iyyar da kintsawa zabubbukan dake tafe.

Dage babban taron dai ya biyo bayan jan kunnen da hukumar zabe ta kasa ta yiwa jam'iyyar ne cewa, bata cika ka'idojin yin taron ba.

Honorable Ali Ndume ya ce za'a gudunar da babban taron a ranar sha shida ga watan satumba.

Da ma dai an zurawa wannan babban taro na jam'iyyar ANPP ido, domin ganin yadda zata warware matsalolin da suka yi mata dabaibayi.