Mutane 140 sun rasu a hadarin jirgin ruwa

Taswirar inda hadarin ya auku
Image caption Taswirar inda hadarin ya auku

Akalla mutane 140 ake kyautata zaton sun rasa rayukansu a wani hadarin jirgin ruwa a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo.

Hadarin ya auku ne a wata magama da ake kira rafin Kasai dake kan kogin Congo, a ranar Laraba. Ministan yadda labarai Lambert Mende ya shaidawa BBC cewar jirgin ruwan ya dauki mutane fiye da kima a lokacin da ya nutse.

Bayan rikice-rikicen da suka addabi kasar tsawon shekaru, ya wancin mutane na tafiya ne a jiragen ruwa, saboda babu hanyoyi masu kyau, da kuma jiragen kasa da ke aiki a kasar.

Mista Mende ya shaidawa BBC cewar ruwan kogin ya yi kasa, abin da kuma ya sanya jirgin ya kife cikin laka.

Ya shaidawa kamfanin dillacin labarai na AFP cewar an samo mutane 76 cikin mutane da ke jirgin da ya kamata ya dauki fasinjoji 180.

Har wa yau dai ya ce ba zai tantance yawan mutanen dake cikin jirgin ba, saboda akwai mutane da ke makare a jirgini ba bisa ka'ida ba.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ce jirgin ya taso ne daga Mushie zuwa Kinsasha, kimanin kilomita 30 daga garin Bandundu.

A watan Nuwamban bara mutane kimanin 73 suka rasu a wani hadarin jirgin ruwa a kogin Mai-Ndombe dake yankin Bandudu.

Jamhuriyar Demodradiyyar Congo kasa ce da za ta kai girman yankin yammacin Turai, amma bata da hanyoyin mota kyawawa in ban da a manyan birane ba. Saboda haka jama'ar kasar ke amfani da jiragen ruwane da kuma kwale-kwale domin yin tafiya mai nisa.