Shugaba mai adalci gaba ya ke da tsarin karba-karba-in ji Dasuki

Taswirar Najeriya
Image caption Najeriya na fuskantar kalubale da dama

A Najeriya,Mai alfarma sarkin Musulmi na goma sha takwas Alhaji Ibrahim Dasuki, ya ce abu mafi muhimmanci ga kasar shi ne samun shugaba mai adalci, ba wai tsarin karba-karba ba.

Alhaji Dasuki ya shaidawa BBC cewa kowa na iya jagorancin kasar,ba tare da la'akari da sashen da ya fito ba.

Ya ce, ''Ni abinda nake so shi ne a samu mutum mai tsoron Allah, wanda zai tsaya ya taimaki kasa,ya yi ayyuka masu kyau. Addu'ar mu ita ce Allah ya bamu shugabanni masu adalci,masu tausayawa talakawa.Allah na iya baiwa kowa''.

Mai alfarma sarkin Musulmi na goma sha takwas,ya koka da yadda shugabannin musamman 'yan siyasa ke wawurar kudaden jama'a, a madadin yin aiki don ci gaban kasa.

Alhaji Ibrahim Dasuki ya soki tsarin siyasar kasar, inda ya ce tsarin bai dace da Najeriya ba.