INEC ta bada wa'adin mako biyu kan kudi

A Nijeriya, hukumar zabe mai zaman kanta, watau INEC, ta ce tana bukatar Naira biliyan saba'in da hudu nan da makonni biyu, domin gudanar da ingantaccen zabe a kasar.

Tun farko dai INEC ta bukaci karin lokaci na kintsawa sosai, sabanin lokacin da sabon kundin tsarin mulkin kasar ya kayyade, na gudanar da zabe a watan Janairu mai zuwa.

A yanzu kuma hukumar zaben ta ce, muddin dai ana son zaben ya zama ingantacce, a wannan wa'adin, to ya zama tilas a ba ta kudaden da ta bukata nan da sati biyu masu zuwa.