Shekaru hamsin:Rashin gaskiya ya yiwa Nijar tarnaki- in ji Conda

Nijar na bikin cika shekaru hamsin da samun 'yanci kai
Image caption Shugaban Nijar,Saliou Djibo

A jamhuriyar Nijar, kakakin majalisar dokokin kasar na farko, Mahaman George Conda, ya ce rashin gaskiya ne ya yiwa kasar tarnaki tun bayan samun 'yancinta shekaru hamsin da suka gabata.

Ya shaidawa BBC cewa tsarin dimokaradiyyar kasar na yanzu, na cike da kura-kurai.

Ya ce:''Babu gaskiyaa kasar(Nijar) kamar yadda ya ke a da.Da kowa ya san iyakarsa, tsakanin nasara da bakin mutum, amma yanzu komai ya sauya.Kaga mutum ba komai ne ba,kafin ya amu mulkin,amma idan aka ba shi wani mukami cikin shekaru biyar sai ya zama mai dukiya.Wannan rashin gaskiya ne''.

George Conda ya yi kira ga shugabannin mulkin sojar kasar su yi amfani da albarkatun kasar wajen ceto ta daga halin yunwar da tsinci kanta a ciki.