Ambaliyar ruwa ta janyo hasarar daruruwan rayuka a Pakistan da Afghanistan

Ambaliyar ruwa a Pakistan
Image caption Ambaliyar ruwa a Pakistan

Ambiliyar ruwa, wadda ruwan saman da ake kamar da bakin kwarya ya haddasa, ta kashe daruruwan mutane a Pakistan da Afghanistan, abinda ya sanya yanki mai yawa kasancewa karkashin ruwa.

Mutane fiye da 400 ne suka mutu a arewa maso yammacin Pakistan, yayin da a Afghanistan makwabciyarta, fiye da mutane 60 suka rasu.

Wasu dubun dubatar mutane kuma sun rasa gidajensu, bayan da koguna suka cika suka batse, inda suka yi awon gaba da kauyuka, da hanyoyi da kuma gadoji.