Isra'ila ta kai mummunan hari a Gaza

Hari a Gaza
Image caption A nan gaba ne ake batun sake cigaba da tattaunawar zaman lafiya

Wasu jerin hare-hare ta sama da Isra'ila ta kai a Gaza sun yi sanadiyar kashe wani babban kwamandan kungiyar Hamas da kuma raunata wasu mutanen su goma sha daya.

Rahotanni sun ce hare-haren da Isra'ilar ta kai suna daga cikin mafiya tsanani a 'yan watannin da suka wuce.

Rundunar soja Isra'ila ta ce hare-haren martani ne ga wani makamin roka da Palasdinawa suka harba a birnin Ashkelon na Isra'ilar a jiya.

Makamin ya fada kan wani gida ne, amma bai raunata kowa ba.