Ambaliyar ruwan Pakistan ta shafi mutane milyan

Ambaliyar ruwa
Image caption An fama da matsalar kai dauki

Majalisar Dinkin Dduniya ta ce ambaliyar ruwa a Pakistan, a sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya, ta shafi akalla mutane miliyan guda.

Ta ce akwai al'umomi da dama da ruwan ya raba su da sauran jama'a, kuma har yanzu ba za a iya tantance girman matsalar ba.

Wani jami'in gwamnati ya ce mutane kimanin dari takwas ne suka mutu a cikin mako gudan da ya wuce.

Akwai kauyuka da gadoji da hanyoyin mota da ruwan ya kwashe yayi gaba da su, baya ga gonaki da suma aka lalata.

Waziz Zada, jami'i ne a hukumar kula da hanyoyin mota a Pakistan, ya ce, “An yi awon gaba da hanyoyin mota masu tsawon kilomita ashirin, haka nan ruwan ya shafe rawul ko randabawul na kimanin kilomita uku, don haka za a kwashe makonni kafin a gyara hanyoyin.

Wani jami’in gwamnatin kuma ya ce mutane kimanin dari takwas ne suka mutu a cikin mako gudan da ya wuce.