Netherlands ta janye dakarunta daga Afghanistan

Dakarun sojan Netherlands sun janye daga Afghanistan
Image caption Yakin na Afghanistan ya yi sanadiyar rushewar gwamnati a Netherlands

A yau lahadi dakarun sojan kasar Netherlands,ke janyewa daga kasar Afghanistan,bayan sun shafe shekaru hudu a kasar.

Duk da ya ke janyewar sojojin ba zata yi wani tasiri mai yawa ba a fannin raguwar sojojin wanzar da tsaron,sai dai masu sharhi kan harkokin kasar na ganin cewa za ta rage kaifin yakin.

Kazalika,janyewar ta girgiza kasashen Turai,musamman kasar Jamus,wadda 'yan adawa suka soka kan shigarta yakin.

Tuni dai kasashen Canada, da Poland suka ce zasu janye sojojinsu.

'Yakin ya jawo rushewar gwamnati a Netherlands'

Rashin jituwa kan ko ya kamata abar sojojin su ci gaba da zama a Afghanistan zuwa badi,ya jawo rushewar gwamnatin hadakar Netherlands,batun da ya tilasta gudanar da sabon zabe a farkon shekarar da muke ciki.