Sudan ta tsaurara wa dakarun wanzar da zaman lafiya

Sudan na sakawa dakarun tsauraran matakai
Image caption Dakarun wanzar da zaman lafiya a Darfur

Gwamnatin Sudan ta ce tana sakawa dakarun kasashen waje da ke aikin wanzar da zaman lafiya a Darfur tsauraran matakai.

Daya daga cikin matakan shi ne,dole ne dakarun su rika yiwa jami'an asirin kasar bayani akan duk wani kai-komo da zasu yi.

Hakan na faruwa ne bayan kisan mutane da dama sakamakon wata kafsawa da aka yi, a sansanin da aka tsugunar da mutanen da yakin basasar kasar ya tagayyara.

Gwamnati ta kara da cewa daga yanzu za a rika bincikar dakarun wanzar da zaman lafiyar a filin saukar jiragen saman Nyala,dake Kudancin Darfur kamar yadda ake yiwa sauran jama'a.

Amma kakakin dakarun wanzar da zaman lafiyar, ya ce bai samu sanarwa daga hukuma ba akan batun.

A makon da ya gabata dai an samu tashen-tashen hankula tsakanin kungiyoyin 'yan tawaye daban-daban a lardin na Darfur.