Holland ta janye dakarunta daga Afghanistan

Sojin Holland
Image caption Canada da Biritaniya ma sun ce za su bi sahu

Kasar Holland ta kawo karshen aikin dakarunta a Afghanistan, bayan shekaru hudu, wadanda a cikin su kimanin dakarunta dubu biyu, suka samu yabon cewa suna cikin wadanda suka fi nuna kwarewa.

Ahmed Joyenda dan majalisar dokoki ne a Afghanistan, ya ce ya kamata kasashe su yi nazari kan ko sun kammala aikin da ya kai su can kafin su janye dakarunsu.

Ya ce, “Ina jin babu makawa kowa zai janye dakarunsa daga Afghanistan, saboda matsin lambar jama'a a kasashensu.

Matsalar a nan ita ce, shin ko hakarsu ta cinma ruwa kuwa kafin janyewar?

Kungiyar NATO ba ta baiwa batun janyewar wani muhimmanci ba, amma masu aiko da rahotanni sun ce janyewar ta zo ne a daidai lokacin da dakarun ke cikin damuwa, a sakamakon karuwar barnar da ake yi masu, da kuma shakku kan salon da ake amfani da shi.

Har wa yau a Afghanistan din, mutane kimanin dari bakwai ne suka yi wata zanga zanga a Kabul, babban birnin kasar a yau, domin nuna rashin amincewa da kisan da sojojin kasashen waje ke yi wa fararen hula.

Bibi Sahari tana daga cikin masu zanga zangar, ta kuma ce, “Mun taru ne domin la'antar muggan matakan da Amurka ke dauka.

“Dakarun Amurka na kashe 'yan Afghanistan a kowace rana, galibinsu mata, ba tare da tantance ko 'yan Taliban ne ba, ko kuma a'a.”

Zanga zangar ta biyo bayan kisan wasu wasu fararen hula sama da arba'in, kwanaki goma da suka wuce, a garin Sangin dake kudancin kasar.