Isra'ilar za ta kori da 'yan ci-rani da 'ya'yansu

Benjamin Netanyahu
Image caption Yana ganin baki za su iya raunana Yahudanci

Gwamnatin Isra'ila ta yi gyara kan wasu matakai dake ta janyo cecekuce, game da fitar da wasu daruruwan kananan yara da wasu ma'aikata 'yan ci-rani suka haifa a cikin Isra'ilar.

Za ta kyale yara da dama da suka rungumi al'adun Isra'ilar su ci gaba da zama, daga cikinsu akwai ke zuwa makaranta da kuma masu jin harshen Hebrew.

Masu aiko da rahotanni na cewa Isra'ilar na son rage yawan dogaro a kan ma'aikata daga waje, ta kuma kare al’ummar Yahudawa daga gurbata da wasu.

Firaminista Netanyahu ya ci bakin haure sun soma yin yawa a kasar. Idan kuma a fitar da su ba, Yahudanci zai yi rauni a kasar.