Manoma sun koka a jihar Kano

Taswirar Najeriya
Image caption Manoma na fuskantar karancin takin zamani

A Najeriya,wasu manoma a jihar Kano, sun zargi gwamnatin jihar da rashin yin adalci wajen rabon takin zamani.

Sun ce gwamnatin na hada jama'a da dama ta basu takin da ba zai gamsar dasu ba.

Wasu manoma a karamar hukumar Kiru dake jihar Kanon, sun shaidawa BBC cewa mutane sama da ashirin ne ake baiwa taki buhu daya.

Sai dai gwamnatin ta ce zargin bashi da tushe balle makama,inda ta kara da cewa tana mu'amala ne da kungiyoyin manoma maimakon baiwa daidaikunsu takin .