Ambaliya ta kashe mutane sama da dubu a Pakistan

Ambaliyar ruwa
Image caption Dubun-dubatar mutane na abukatar agaji

Jami'ai a Pakistan sun ce mutane sama da dubu daya da dari daya ne suka mutu a ambaliyar ruwa mafi muni da aka taba gani a kasar cikin shekaru aru-aru.

Dakaru sama da dubu talatin ne aka nemi gudunmawarsu wajen ayyukan ceto, inda suke kokarin kaiwa ga wadanda abin ya rutsa da su domin kai masu kayan agaji.

Manjo Janar Athar Abbas, shi ne kakakin sojin kasar ta Pakistan.

Ya kuma ce, ”Barnar tana da girma kuma ta watsu zuwa wurare da dama, ta yadda mai yuwuwa akwai wasu karin yankunan da aka samu barna da kuma asarar rayuka, wadanda ba a bada labari ba.”

'An bude wasu sassan babbar hanyar kasar'

An bude wasu sassan babbar hanyar kasar dake yankin arewa ta yadda za a iya zuwa sauran bangarorin na Pakistan.

Akwai wani jirgin kasa dake wannan yanki inda 'yan kasuwa ke ta hakilon kai kayayyaki kasuwanni don sayarwa.

Sannan kuma iyalai na dokin haduwa da 'yan uwansu.

Mutanen yankunan da ambaliyar tafi yin barna kuwa na tare da dabbobinsu,inda suke neman taimako.