Gudanar da zabe a lokuta daban daban zai hana magudi-in ji 'yan Najeriya

Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta,Farfesa Attahiru Jega
Image caption Hukumar zaben ta sha alwashi gudanar da zabe mai sahihanci a shekarar 2011

A Najeriya,wasu 'yan kasar sun bayyana cewa hanyar da za a bi don kaucewa magudin zabe ita ce gudanar da shi a lokuta daban-daban a shiyoyi shida na kasar.

Sun ce gudanar da zaben a lokuta daban-daban, zai baiwa jami'an tsaro da kuma jam'iyyun siyasa damar tura wakilansu kowanne sako na kasar don tabbatar da adalci,sabanin abinda zai faru idan aka gudanar da shi lokaci guda.

Fasfesa Obasi Igwe,wani masanin siyasa ne,kuma ya ce, ''mun gano cewa gudanar da zabukan a lokuta daban-daban shi yafi A'ala a Najeriya,domin idan aka gudanar da su a lokuta guda,abu ne mai sauki a tafka magudi''.

Kazalika,masu wannan ra'ayi na ganin cewa gudanar da zabukan a lokuta mabambanta zai baiwa hukumar zaben kasar damar kidaya duk kuri'un da aka kada yayin gudanar da zabe,ba tare a zargin kunbiya-kunbiya ba.