Likitoci sun fara yajin aiki a jihar Borno

Wasu marasa lafiya da ake jinya a Nijeria
Image caption Wasu marasa lafiya da ake jinya a Nijeria

A yau ne Likitocin jihar Borno dake arewacin Nijeria suka fara wani yajin aikin sai baba ta gani a bisa dalilan da suka bayyana na rashin biya musu bukatun su daga gwamnatin jihar.

Wadannan bukatu kuwa sun hada da batun biyan sabon tsarin albashin likitocin wato CONMESS, da sauran matsalolin da suka dade suna damun su.

Sun hada da rashin kyautata jin dadin likitocin kamar karin albashi da alawu-alawus da yanayin aiki da makamantansu, wadanda suka bayyana cewar takwarorin su da dama a wasu jihohin suna amfana.

Wannan yajin aikin zai iya haifar da karuwar matsalolin kiwon lafiya ga jama'a musamman masu karamin karfi da suka dade suna fuskanta a jihar.