Dakarun Amurka za su bar Iraqi a karshen watan nan

Shugaba Obama
Image caption Shugaba Obama

Shugaba Obama ya tabbatar da cewar za a janye dukanin dakarun Amurkan dake yaki daga Iraqi nan da karshen wannan wata na Ogusta.

Da yake magana a wajen taron nakassasu 'yan mazan jiya a Atlanta, ya ce wannan zai kasance cika alkawarin da yayi ne jim kadan bayan da ya dare kan karagar mulki.

Dakarun Amurka dubu 50 ne daga cikin dubu 65 da a halin yanzu ke Iraqi za su ci gaba da kasancewa a kasar har ya zuwa karshen shekara mai zuwa domin horadda dakarun Iraqi da kuma taimakawa ga ayyukan yaki da ta'addanci.

Wakilin BBC a Bagadaza ya ce wasu 'yan Iraqi na nuna damuwa cewar hare haren kungiyar Al -Qa'ida na karuwa yayinda Amurkawan ke ficewa.