Binciken kashe 'yan Turkiyya: Isra'ila za ta ba da hadin kai

Gwamnatin Isra'ila ta ce za ta bayar da hadin kai ga wani bincike na Majalisar Dinkin Duniya game da farmakin da Isra'ilar ta kai a kan wani ayarin jiragen ruwa dake dauke da kayan agaji zuwa Gaza cikin watan Mayu inda wasu yan kasar Turkiyya tara suka rasa rayukansu.

Firaminista Benjamin Netanyahu, ya ce Isra'ila ba ta da wani abu na boyewa.

A baya dai Isra'ila ta ce babu wani dalili na gudanar da wani binciken kasa da kasa a kan lamarin.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-Moon yayi marhabin da sanarwar ta Isra'ila.

Ya ce wannan wani abu ne sabo cewar zamu kafa wannan kwamitin bincike.

ya kara da cewa zai dauki wannan dama domin godewa shugabannin Isra'ila da Turkiyya saboda kokarinsu na sasantawa da kuma halayyar tarar gaba.

Turkiyya dai ta yi marhabin da binciken na Majalisar Dinkin Duniya, wanda ta gindaya a matsayin wani sharadi a duk wata yiwuwar ingantuwar dangantaka da Isra'ila.

Kasashen biyu a da muhimman kawaye ne.