Gurbacewar yanayi da zaizayar kasa a jamhuriyar Nijar

Image caption Zai zaiyar kasar ta haddasa fari da karanci abinci

Shekaru aru-aru a kasashen kudu da hamadar Sahara dan adam ya kwashe yana rayuwarsa bilbishin kasa tare da albarkatu masu yawa da Allah ya shinfida a doron kasa ba tare da tunanin karewar albarkatun ba.

Haka dai zancen yake a jamhuriyar Nijar inda mutane da dama suka maida sarar itatuwa sana'a.

Hakan ya sa kowace safiya dubban itace ne ake kashewa dan biyan wasu bukatu na gida. Idan aka dubi yanayi a shekaru talatin din da suka gabata da wannan lokaci za'a gano cewa akwai banbancin gaske.

To sai dai a cewar masana kan harkar raya gandun daji akwai damuwa sosai kan batun canjin yanayin da a cewar masu nazarin, mutane ne tushen wannan lalacewar yanayi.

Kasar Nijar na fama da matsalar gurbacewar yanayi da zaizayar kasa wanda a cewar masana yana da nasaba da abubuwa uku.

Na daya akwai hanyar da mutane ke sarar daji da zummar kara girman gonakinsu, na biyu akwai kiwo, ganin yadda mutane suka mallaki bisashe da dama, na ukun su shi ne wutar daji masanan sunce mutane na cinnawa ciyawa wuta.

Masu nazari kan al'amuran yau da kullum na hasashen cewa da zarar gwamnati bata yi wani abu ba wajen hana sarar daji da itatuwa to tabbas akwai matsalar gaske ta yanayi da za'a fuskanta nan gaba .

Ko da yake malama Mariama wata mata ce 'yar kasar ta Nijar cewa tayi basu da halin sayen fetur ko gas dan domin girki ganin kasar Nijar kasa ce matalauciya.

Shi ma malam Kalla cewa yayi ganin yanda iyalai ke dada yawa ya zama wajibi ga magidanta su kara fadin gonakinsu .

A bin da ya shafi matsalar yanayi da zaizayar kasa har yanzu dai ana iya cewa kasar Nijar na lalube cikin duhu wajen gano bakin zaren.