Yadda matasa ke fita ci rani a Nijar

Noma a Nijar
Image caption Noma da kiwo shi ne madogarar tattalin arzikin jama'ar Jamhuriyar Nijar

Ci rani ko dandi ba bakin kalmomi bane ga majiya karfi a kasar Nijar. Tun ba yau bane matasan ke barin gida da zummar zuwa wasu kasashe, domin ci rani.

Irin kasashen da suke zuwa sun hada da birnin Abidjan na kasar Ivory Cost da Lagos a tarrayar Najeriya da zumar neman na sama bakin salati bayan kimshe cimaka an kuma adana kafin wata damana ta kewawo.

To sai dai abun ba haka yake ba yanzu domin Matasan kasar ta Nijar sun dandana dadin kwarara kasashen Turai ta jirgin ruwan daga Libiya ko Aljeriya.

Abin da ba karamin aiki ba ne, ganin yadda wani lokacin matasa da dama ke rasa rayukansu kan hanya.

Har ila yau wasu kan rasa yukan na su ne cikin hamadar sahara kafin shiga kasar ta Libya.

Sauyin zamani

Wani magidanci a garin Maradi, Alhaji Saidu, ya shaidawa BBC cewa lokacin da abin duniya na madara wato lokacin da Nijar ke cikin wadata ne yake zuwa ci rani.

Ya ce suna yin hakan ne dan galari ganin abokai sun fita kai ma sai ka shirya jakarka, sai ya kara da cewa: "Da ance an samu ruwa sai kowa ya koma gida".

Amma a cewar wani matashi mai suna Rabe wanda ya dawo daga Libya kwanakin nan, yanayin da kasar ta Nijar ke ciki a yanzu, yasa ba za su iya bin sahun magabatansu ba.

Ya ce a wancan lokacin kasar nada sauran albarkatun kasa, amma yanzu wahala ce kawai ta rage.

Wani bincike da BBC ta gudanar ya nuna cewa bayan samun 'yancin kai daga turawan milkin mallaka, kasar Nijar na daukar dawainiyar 'ya'yanta ta kowanne fanni ka ma daga ilimin kiwon lafiya, da dai sauransu.

Hakan ne kuma yasa wasu har suka koma ga mahalacinsu ba su san fita daga kasar.

Yayin da a wannan lokaci, daidai da biro a makaranta ko maganin ciwon kai a asibi sai mutun ya saya, hakan na tunzura matasa da magidanta da dama.

'yan Nijar na haurawa ci rani zuwa kasashe kamar Najeriya da Libya

Sai dai a nata bagare gwamnatin kasar ta idan danbu yayi yawa baya jin mai, amma duk da hakan tana iya kokarinta domin ganin ta fita hakin dukkan 'yan kasar.

Kuma ta ce tana yin hakan ne ta hanyar kirkiro da ayyukan yi, bada kudaden bashi ga mata da matasa domin dogaro da kai da kyautata makomar karatu da inganta asibitoci da dai sauransu.

Masu lura da al'amura da dama na danganta kaurar da jama'ar kasar ta Nijar dama na wasu kasashen Afrika ke yi, da karancin kayayyakin more rayuwa, wanda masana ke alakantawa da cin hanci da rashawa da ake zargin shugabannin kasashen da aikatawa.