An kai wasu tsoffin jami'an Nijar kotu

A jamhuriyar Nijar, dazu ne aka kai tsohon praministar kasar, kuma shugaban jam'iyyar MNSD Nasara, Seini Umaru gaban wata kotun majistare a Yamai.

Ana shirin gabatar da su ne a gaban kotun tare da Malam Saleh Habi, mataimakin shugaban jam'iyyar MODEN-Lumana, da kuma wani tsohon darakta a ma'aikatar makamashi ta kasar.

A makon da ya gabata ne aka kama su, bisa zargin karkata wasu kudade, a ma'aikatar kasuwanci ta kasar a can baya.

Malam Seini Umaru, da Malam Saleh Habi dai kowannensu ya taba rike mukamin minista a ma'aikatar.