Ambaliyar ruwa ta ci mutane a Pakistan

barnar ambaliyar ruwa a Pakistan
Image caption barnar ambaliyar ruwa a Pakistan

An yi alkawarin bayar da miliyoyin daloli na agaji ga Pakistan inda mutane fiye da dubu daya suka mutu sakamakon wata ambaliyar ruwa mafi muni a cikin shekaru da shekaru.

Majalisar Dinkin Duniya za ta bayar da gudummawar dala miliyan goma.

Amurka kuma ta bayyana bayar da wata dalar miliyan goma da helikwabtoci da kuma kwale kwale.

Mutane fiye da miliyan daya da rabi ne aka yi kiyasin suna bukatar taimako a arewa maso yammacin Pakistan.

Kakakin kungiyar bayar da agaji ga yara ta Save the Children ya shaidawa BBC cewar a daya daga cikin yankunan da lamarin ya fi kamari, Kwarin Swat da wuya tawagogin su samu sukunin kai taimako can.