Kotu ta saurari karar kwakulewa yaro ido a Kaduna

A yau ne wata kotun majistare dake Kaduna ta saurari wata kara ta kwakulewa wani yaro almajiri idanuwa.

Ana zargin wasu mutane biyune da hada baki da kwakulewa wannan yaro almajiri dan shekaru 10 idanuwa domin yin tsafi.

A zamanta na yau kotun ta amince da canza tuhumar da ake yiwa wadanda ake zargin da hada baki dan jiwa wani rauni ya zuwa hada baki da jiwa wani rauni da kuma kokarin yin kisan kai.