An gwabza tsakanin Isra'ila da Lebanon

Sojin Lebanon yana jan daga
Image caption Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiran taka-tsantsan

An gwabza tsakanin sojin |sraila da Lebanon a kan iyakar kasashen biyu.

Musayar wutar ta yi sanadiyyar rasuwar wani babban jami'in sojan Israila da kuma sojojin Lebanon biyu da dan jarida guda.

Jami'an Lebanon sun ce dakarun Israila ne suka keta iyakar Lebanon din domin sare wata bishiya da ke tare gaban wata kyamararsu ta leken asiri.

Sai dai kakakin sojin Israila Manjo Janar Gadi Eizenkot ya musanta zargin.

Ya ce, “A fahimtarmu wannan shiryayyiyar makarkashiya ce daga bangaren Lebanon, kuma takalar fada ne ba tare da wani dalili ba.”