Jamhuriyar Nijar ta cika shekaru hamsin

Jamhuriyar Nijar ta cika shekaru hamsin
Image caption Jamhuriyar Nijar ta cika shekaru hamsin da samun 'yan cin kai, sai dai akwai kalubale da dama a gaban kasar

A ranar Talata ne jamhuriyar Nijer ke cika shekaru 50 da samun 'yan cin kai daga Turawan mulkin mallaka na kasar Faransa.

Galibi kasashen da suka kai wadannan shekaru dai na tsara kasaitattun bukukuwa don bayyana murnar cika wadannan shekaru na 'yanci.

Bukin na bana ya zo wa jamhuriyar ta Nijer cikin wani mawuyacin hali sakamakon matsalar karancin abinci da kasar ke fama da ita, ga kuma matsin tattalin arziki.

Kungiyar agaji ta Save the Children, ta ce akalla mutane miliyan takwas ne ke bukatar taimakon abinci a kasar, sakamakon mummunan farin da kasar ta yi fama da shi. Haka kuma bikin ya zo ne a lokacin da sojoji ke mulkin kasar, abin da yasa wasu ke ganin ka iya rage armashin bikin.

Tarihi

Jamhuriyar Nijar ta samo sunan ta ne daga kogin Naija duk kuwa da cewa ba ta kusa da wata babban mashigin ruwa. Nijar na makwabtaka da Najeriya da Benin ta kudanci, Burkina Faso da Mali ta yammaci, Aljeriya da Libiya ta arewaci, sai kasar Chadi ta bangaren gabas.

Image caption Jamhuriyar Nijar ta fuskanci kalubale da dama

Kodayake sai a cikin karni na goma sha tara ne Turawa kamar Mungo Park dan kasar Burtaniya, suka fara shiga can bangaren kogin Naija, to amma dai tun kafin wannan lokacin Faransa ke ta kokarin ganin ta mallaki Nijar, inda ta samu nasara a shekarar 1890.

A wannan lokaci Faransa ta na da gwamnonin dake tafiyar da harkokin dukkanin yankunan da ta mamaye a yammacin Afirka ciki harda Nijar, wadanda ke aiki karkashin babban gwamna, wanda ke zaune a Dakar na kasar Senegal.

Ranar goma sha takwas ga watan Disambar shekarar 1958, Niger ta zamo Jumhuriya mai cin gashin kanta a karkashin ikon Faransa.

Sannan a ranar uku ga watan Agusta na 1960, jamhuriyar Nijar ta samu 'yancin kai, wato shekaru hamsin da suka wuce.

Kalubale

Jamhuriyar Nijar ta yi fama da juyin mulki daga sojoji daban daban wadanda suka mamaye madafen iko a kasar bayan ta samu 'yancin kai.

Kasar wacce ke fama da matsanancin fari, na fadi-tashin ciyar da jama'arta.

Babban abin da take fitarwa dai shi ne ma'adanin Uranium wanda shi ma a shekarun baya ya fuskanci rashin tabbacin farashi, yayin da kwararowar hamada ke barazana ga aikin noma.

Image caption Sojoji da dama ne suka mulki jamhuriyar Nijar tun bayan samun 'yancin kai

Amma a gefe guda kasar na fatan fara hako man fetur wanda ka iya bunkasa tattalin arzikinta.

Bayan samun 'yancin kai, kasar ta fuskanci mummunan fari wanda ya lalata albarkatun noma.

Kasar dai ba ta da wani tsarin ilimin Firamare na azo a gani, abin da ya sa take cikin jerin kasashen da ke fama da rashin ingantaccen ilimi a duniya.

Harkar lafiya ma ba ta da kyau sosai, kuma akwai yaduwar cututtuka a ko'ina cikin kasar.

A lokuta da dama kasar ta yi fama da boren 'yan tawayen Abzinawa a Arewacin kasar.

Sai dai a shekara ta 2009, gwamnati da 'yan tawayen sun sanya hannu kan yarjejeniyar samar da zaman lafiya a birnin Tripoli na kasar Libya.