Tarihin Matsalar karancin abinci a jamhuriyar Nijar

Tarihin Matsalar karancin abinci a jamhuriyar Nijar
Image caption Nijar ta dade tana fama da matsalar yunwa

An fara samun karancin abinci a Nijar a karon farko a shekara ta 1970, shekaru goma bayan samun yancin kai daga turawan mulkin malaka.

Shekaru hudu bayan hakan kuma kasar ta sake fadawa cikin wani hali kuma yunwar ta zo dai dai lokacin da sojoji suka kwace mulki a lokacin inda kuma Marganyi tsohon shugaban kasar Saini kunce ya yi alkawarin cewa ba dan nijar din da zai mutuwa da yunwa ko da kishin ruwa sai dai ta mai dauka ba ta mutun ba .

Shekaru goma gaba kuma kasar ta Nijar ta sake abkawa cikin bala'in yunwa a shekarar 1984, a wannan lokacin ma matsalar ta munana inda duban dabobi ne suka halaka sakamakon hakan.

Binciken da aka yi, ya hada ne har da yadda kananan yara 'yan kasa da shekaru biyar suke fama da karancin abinci ko ma suke fuskantar barazanar mutuwa a sakamakon yunwa.

Mafi yawan bayanai da alkaluman da aka yi amfani dasu, sun samu ne tun a shekara ta 2005.

Hakan ya sanya a kasar Nijar mai, mutane akalla miliyan uku su ka kasance su na dogaro kan taimakon abinci daga ketare.

Iris Krebber wata jami'ar kungiyar Red cross ta ce, matsalar na tasowa sannu a hankali, wadda kuma ba'a cika maida hankali a kanta ba.

Sai kuma a shekara ta 2010 lokaci ya maimaita kansa, sai dai abunda za'a kwatanta wannan yunwa data dubu biyu da biyar shi ne yadda yara kanana ke karo da ajalin su sakamakon wannan matsananciyar yunwa .

A kalla mutane milliyan bakwai ne da dubu dari biyar ke dandana kudar su a wannan shekara kuma tuni milliyoyin dabbobi ne ake kyautatta zaton cewa sun mutu sakamakon yunwa.

Malama Iris ta kara da cewa "A ra'ayi na, a yankuna da dama, mun kai matsayi na kaka-ni-kayi. A halin da ake ciki gaba daya, ana iya cewar an sami barnar da nan da shekaru goma masu zuwa ma, sai an zuba jari mai dimbin yawa da karfin zuciya mai yawa da aiki tukuru sa'annan za'a shawo kanta".

Kungiyar agaji ta Concerne ta ce za ta maida hankalin ta ga wannan aiki, musamman a bangaren taimakawa mata, saboda nazarin da aka yi ya nuna cewar mata ne suka fi fama da matsalar yunwa fiye da takwarorin su maza.

Wani abu da yake nuni da girman matsalar, shi ne yadda lamarin ya kara tsananta a karshen 2011 har zuwa farkon shekarar 2012.

Wannan ya sanya gwamnatin ta Nijar fitowa fili ta nemi agajin kasashen duniya bayan da ta bayyana cewa wasu sassan kasar na fama da matsalar karancin abincin.

Masu lura da al'amura na ganin akwai bukatar kasashen duniya su tashi tsaye idan har anaso a shawo kan wannan matsalar, musamman ta hanyar tallafawa matan da mazajensu ke tafiya su barsu a cikin mawuyacin hali.

Rahoton Kungiyar agaji ta Concerne ya ce wajibi ne a kawar da matan na nahiyar Afrika daga halin da su ke ciki na rayuwa cikin wahala. To amma wannan ba abu ne mai sauki da zai yiwu cikin dare daya ba.