Nijar ta shekara 50

Salou Djibo
Image caption Za a kara maida hankali ga noma

Yau ne Jumhuriyar Nijar ta cika shekaru hamsin da samun mulkin kai daga kasar Faransa.

Hukumomin kasar sun takaita shugulgulan bikin wannan rana.

Ta kuma yi wani bukin dashen itatuwa da kuma jawabai ga ‘yan kasa, akasin bukukuwan ire-iren wadannan ranaku a shekarun baya.

A jiya da dare shugaban kasar, Janar Salu Jibo ya yi wani jawabi ga al'ummar kasar, inda ya tabo batutuwa da dama.

Ciki akwai irin yadda kasar za ta gyara sha’anin nomanta, yadda za kauce wa ci gaba da aukuwa cikin yunwa duk bayan shekaru.