An kashe mutane 35 a Pakistan

Rikicin Pakistan
Image caption An dade ana fama da rikicin kabilanci da siyasa a garin Karachi

A kalla mutane 35 ne suka rasa rayukansu bayan da tashin hankali ya barke a garin Karachi na Pakistan, sakamakon kisan wani dan siyasa Raza Haider, ranar Litinin.

Titunan birnin duka sun dade, yayinda 'yan bindiga ke ci gaba da kaiwa da komowa a ciki da wajen birnin.

Mista Haider, wanda ke da tasiri sosai a jam'iyyar MQM, an kasheshi ne a lokacin wata jana'iza da aka gudanar a wani masallaci - jam'iyyarsa ta zargi abokiyar hamayyarta ta ANP da hannu a kisan.

Wakilin BBC ya ce an dade ana zubda jini a garin Karachi, inda ake fama da banbance-banbancen kabilanci da na addini.

Kungiyoyin kare hamkkin bil'adama sun ce fiye da mutane 300 ne suka hallaka sakamakon rikice-rikicen da ke da alaka da siyasa a garin na Karachi a bana.

Martani

Tuni dai jam'iyyar ta ANP ta musanta zargin cewa tana da hannu a kisan.

Jama'ar garin sun yi hasashen rikicin ka iya barkewa, domin tun da farko suka rufe shaguna da kasuwanni, sannan suka garzaya gidajensu.

Jam'iyyun biyu dai na da tasiri sosai a yankin inda kuma banbancin addini ya ke musu tasiri sosai.

Ita dai jam'iyyar MQM ta 'yan shi'a ce yayinda a daya bangaren jam'iyyar ANP ke bin tafarkin Sunna.

Wannan rikicin na zuwa ne adaidai lokacin da mahukunta ke kokarin shawo kan mummunar ambaliyar da ta afkawa kasar bayan shafe kwanaki ana tafka ruwa kamar da bakin kwarya.

A yanzu dai an kiyasta cewa sama da mutane 1,000 ne suka rasa rayukansu, a wannan bala'in. Yayinda abin ya ritsa da fiye da miliyan biyu.