Ga alamu kamfanin BP na samun nasara

Wajen hakar mai na BP
Image caption Babu daya daga cikin masu aiki a wurin da ke da tabbasa za a yi nasara

Kamfanin mai na BP ya bayyana cewa ya fara yunkuri na baya-bayan nan na like rijiyar mansa da ke Tekun Mexico, kwanaki dari bayan rijiyar ta fara kwararar da miliyoyin gangunan danyen mai a ruwan Tekun.

Masana kimiyya da injiniyoyi na amfani ne da wata dabara ta cusa tabo cikin rijiyar daga saman ruwan don like rijiyar.

Sai dai babu daya daga cikin masu aikin toshe rijiyar man na BP da zai iya bugun kirjin cewa aikin zai yi nasara—ba za a iya sanin ko dabarar ta yi aiki ba sai nan da mako guda—to amma mai yiwuwa kamfanin ya kusa kawo karshen kwararar da danyen man fetur din ke yi.

Aikin dai ya fara nisa, kuma akwai alamun komai na tafiya yadda aka tsara.

Image caption Taswirar hanyar da kamfanin BP yabi wajen shawo kan matsalar kwararar mai

Wannan kuwa na zuwa ne bayan gwamnatin Amurka ta bayyana cewa wannan ce kwararar mafi muni a tarihi.

Irin wannan dabarar ce dai aka yi amfani da ita a watan Mayu ba a yi nasara ba.

To amma a wannan karon an saka wani marufi a bakin rijiyar wanda ya yi makwanni biyu ba tare da ya motsa ba.

Ko da an yi nasarar kawo karshen al'amarin dai, za a jima ana jin radadin illar da kwararar man ta haifar.

Tattalin arzikin yankunan da abin ya shafa dai ya gurgunce, yayin da wasu iyaye ke kai rahotannin matsalolin da suka shafi lafiya da ma dabi’un 'ya'yansu.