Shakku kan harin da aka kaiwa Shugaban Iran

Muhmud Ahmadinejad
Image caption Shugaba Ahmadinejad ya dade yana fuskantar kalubale daga ciki da wajen kasar

Ana samu rahotannin masu karo da juna daga ofishin shugaba Ahmadinejad na Iran, bayan da aka kaiwa tawagarsa hari ranar Laraba a Yammacin kasar.

Rahotanni na baya bayan nan sun rawaito jami'an Iran suna cewa babu wani hari da aka kaiwa shugaban.

Gidan talabijin na kasar ya zargi kafafen yada labarai na kasashen Yammacin duniya da yada labarin, wanda yace ba shi da tushe.

Tun da farko sashin intanet na masu ra'ayin rikau ya tabbatar da harin, amma yace babu abin da ya samu shugaban.

Gidan talabijin na Lebanon da ke Dubai Al Arabiya, ya ambato jami'an ofishin shugaban kasar suna tabbatar da bayanan.

An ce maharin ya jefa bom kan tawagar shugaban, kafin daga bisani a kamashi.

Rahotanni sun ce wasu mutane sun jikkata a harin.

Shugaban dai ya bayyana a gidan talabijin na kasar, yana jawabi ga jama'a a wani filin wasan kwallon kafa, sai dai bai nuna alamar an kai masa wani hari ba.

A ranar Litinin ne dai shugaban ya yi zargin cewa Yahudawa na kokarin hallaka shi.