Aikin idanu kyauta a Jigawa

Likitan idanu
Image caption Likitan idanu

Gwamnatin Jihar Jigawa tare da hadin guiwar kungiya mai yaki da cutar makanta mai suna vision 2020 sun gudanar da wani aiki ga wasu mutane da dama wadanda ke fama da yanar ido.

Kungiyar Vision 2020 wadda keda hedkwatarta a jihar Plateau suna gudanar da aikin yiwa masu fama da cutar yanar ido magani kyauta ne.

Ana dai gudanar da aikin ne a cibiyoyi 5 na jihar.

Gwamnatin jihar Jigawa ta kulla yarjejeniya ne tare da kungiyar domin yin wannan aiki sau uku a kowace shekara.

Wannan kuma shi ne zagaye na biyu a bana. A kowane zagaye dai ana yiwa mutane kusan dubu daya ne aikin.

Mutane da dama sun bayyana farin cikinsu akan yadda a yanzu suna iya gani, bayan da suka shafe shekaru masu yawa basa iya gani.