An fara kada kuri'ar raba-gardama a Kenya

Masu adawa da sabon tsarin mulkin Kenya
Image caption Masu adawa da sabon tsarin mulkin sun ce zai kara rikirkita al'amura ne kawai

Mutanen Kenya da dama ne suka yi tururuwa zuwa rumfunan zabe don kada kuri'a a wani zaben raba-gardama a kan ko za a amince da sabon kundin tsarin mulkin kasar.

Karfe shida da 'yan mintuna na safiya jami'in zabe ya bude zauren tunawa da MV Patel da ke Eldoret.

Bude zauren ke da wuya, sai dimbin mutanen da suka yi jerin gwano a bakin kofa suka barke da sowa.

Wadanda ke kan gaba a dogon layin masu kada kuri'ar sun bayyana cewa tun karfe biyun dare suka hallara.

Kusan dukkan mutanen da wakilin BBC ya tattauna da su dai sun bayyana cewa sun hakikance za a amince da sabon kundin tsarin mulkin.

Shi dai sabon kundin tsarin mulkin shi ne kashin bayan sauye-sauyen da aka tsara don gujewa sake aukuwar tashe-tashen hankulan da suka biyo bayan zabukan da aka gudanar a watan Disamban 2007.

Sai dai wadanda ba sa goyon bayan sabon kundin tsarin mulkin sun ce zai kara rikirkita al'amura ne kawai.

Eldoret dai na cikin wuraren da tashe-tashen hankulan suka fi kamari, kasancewarsa cibiyar 'yan adawa, kuma irin shaukin da mutanen garin ke da shi na nuni da cewa kuri'ar jin ra'ayin jama'ar da aka gudanar ka iya tabbata, wato mutanen Kenya za su amince da sabon kundin tsarin mulkin.