Kuri'ar rabagardama a Kenya

Wata alama dake nuna hanyar zuwa rumfar zabe
Image caption Wata alama dake nuna hanyar zuwa rumfar zabe

Mahukuntan Kenya sun ce su na da kwarin gwiwar al'ummar kasar za su amince da sabon tsarin mulki a kuri'ar raba gardamar da su ke kadawa a yau.

Mutane da yawa ne suka yi tururuwa zuwa rumfunan zabe a kasar domin kada kuri'unsu.

An dai shirya kundin tsarin mulkin ne domin daidaita siyasar ta Kenya da kuma kaucewa irin rikicin da ya biyo bayan babban zaben da aka yi a watan Disamban 2007, inda aka kashe fiye da mutane dubu daya.

Firaministan Kenyan, Raila Odinga ya ce wannan rana ce mai muhimmanci a tarihin Kenya saboda an ba al'ummar kasar damar zabar makomar da suke bukata.