Ana gab da magance matsalar malalar Mai

Shugaba Obama
Image caption Shugaba Obama

Shugaba Obama na Amurka ya ce an kusa kawo karshen tashi fadin da ake yi wajen dakatar da kwararar da mai ya ke yi a tekun Mexico.

Gwamnatin Obama ta ce galibin man da ya kwarara daga tashar hako mai ta kamfanin BP a tekun Mexico, ya bace daga saman teku.

Wani rahoton gwamnatin Amurka ya ce an kwashe kaso uku cikin hudu na man da ya malala, wani kuma ya zama tururi ya bi iska.

Sai dai rahoton ya yi gargadin cewa gabar kogin da ke yankin na fuskantar barazanar gurbacewa amma kawo yanzu ba'a tantance irin illar da lamarin ya haifar ba.

To saidai duk da haka har yanzu akwai sauran Mai da yawa a can karkashin tekun.

A can baya a wani yukuri na magance bul-bulowar Man, an fesa wani sinadari mai kama da Omo akan man a daidai lokacin da ya ke fitowa daga bakin rijiyar.

To saidai a madadin yin hakan ya sa man ya malala, sai kawai ya dankare a karkashi ruwa, inda yanzu haka akwai Mai dunkule da iskar gas da kuma sinadarin da aka fesa a karkashin tekun.